Adon Cikin Gida (Interior Design)

Write your awesome label here.
  • Malama: Khadija Yaya
  • Mataki: Na tsakiya
  • Babi: 11
GAME DA DARRASI
Adon gida da fili abune da ke kara kyan wuri amma ba kowa yasan yanda akeyi ba. Tabbas kyale gida ya fito yayi ras yana daya daga cikin abunda mace yakamata ta koya. Wannan darasin ya zo muku da abubuwa da dama na adon cikin gida fara daga yanda ake gyara filin gida daga farko har karshe har yanda zakuyi amfani da haske wajen kawata cikin gidan ku.

TAKKARDAR KAMALAWA
Wannan darasin yana zuwa tare da Takaddar kammalawa wanda DG-SMEDAN ya sanya hannu, kuma zai iya zama ɓangare na Takaddun Kasuwancin ku, kuma ya ƙirƙirar ƙarin dama ga kasuwancin ku. Za'a iya raba Takaddun a kan Linkedin ko Facebook ko Twitter kai tsaye daga shafin yanar gizon ku.

Wanna darasin na ƙunshe da abubuwan da ya kamata ku sani game da adon cikin gida da yanda za a sarrafa wasu abubuwan adon cikin gida ba tare da an sayo su a kasuwa ba, abubuwa kamar su pilon jerawa a  palo da bargon yara da dai sauran su

A wannan darasin za a koyi yanda ake ƙawata kayan adon cikin gida domin kwalliya. za a koyi yanda ake haɗa pilo, bargon yara, ire-iren kayan kwalliyan bango, da yanda ake amfani da haske da sauransu.
Meet the instructor

Khadija Yaya

Khadija yar makarantar jami'a ce wanda take samun nishadi wajen yin kayan adon gida da kuma piluluka. Ta kwashe shekaru masu yawa tana yin sana'ar adon cikin gida. Tayi wannan darasin ne domin koyar da mutane sana'ar adon gida da fili domin ilimantar da al'uma.
Patrick Jones - Course author