Bunkasa Kai (Personal Development)

Write your awesome label here.
  • Malama: Halima Abdulra'uf
  • Mataki: Na tsakiya
  • Modules: 3
GAME DA DARASI
Da yawan mu, muna son dogara da aikin gomnati wanda yanzu samun aikin ta yi ƙaranci a kasar mu Najeriya. Akwai abubuwa da dama da zaka yi domin ganin ka gina kanka. A wannan darasin zamu duba yanda mutum zai ci gaba da bunƙasa rayuwarsa ta koyan aikin hannu, sana'a, kwaikwaiyar ɗabi'u masu kyawu tare da yin taka-tsantsan da muradunsu na rayuwa domin cimma nasara.

TAKKARDAR KAMALAWA
Wannan darasin yana zuwa tare da Takaddar kammalawa wanda DG-SMEDAN ya sanya hannu, kuma zai iya zama ɓangare na Takaddun Kasuwancin ku, kuma ya ƙirƙirar ƙarin dama ga kasuwancin ku. Za'a iya raba Takaddun a kan Linkedin ko Facebook ko Twitter kai tsaye daga shafin yanar gizon ku.

Wannan darasin yana ƙunshe da bayanai dalla-dalla akan yanda mutum zai ci gaba da bunƙasa rayuwarsa ta koyan aikin hannu, sana'a da sauransu.
A wannan darasin zaku koyi bunƙasa rayuwarku ta hanyar koyan aikin hannu, sana'a, kwaikwayon ɗabi'u masu kyau tare da yin taka-tsantsan da muradunku na rayuwa domin cimma nasara.
Meet the instructor

Halima Abdulra'uf

Halima Abdulra'uf matashiya ce kuma kwararriyar yar jarida. Ta kwashe shekaru aƙalla goma tana aikin jarida. Duba da yanda matasan mu ke zaune babu aikin yi ba sana`a don jiran aikin gomnati, shine ta zo da wannan darasin ɗauke da hanyoyi da dama da zaka bunƙasa kanka don ganin ka samu abun yi ba tare da jiran gomnati ba.
Patrick Jones - Course author